Kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Usman Ankwai, ya rasu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Ankwai ya rasu ne a daren ranar Litinin, bayan fama da rashin lafiya, yayin da yake karɓar magani a Masar.
Marigayin, wanda ke wakiltar mazabar Zuru a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan siyasa masu tasiri a jihar Kebbi.
Rasuwarsa ta jawo alhini daga shugabanni, ‘yan majalisa da kuma al’ummar jihar, yayin da ake ci gaba da jiran sanarwa a hukumance kan shirye-shiryen jana’izarsa.