Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

ADC ta zargi INEC da yunkurin hana ta shiga zaɓen 2027

ADC ta zargi INEC da yunkurin hana ta shiga zaɓen 2027 ADC ta zargi INEC da yunkurin hana ta shiga zaɓen 2027
ADC ta zargi INEC da yunkurin hana ta shiga zaɓen 2027

Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC da shirin hana ta tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar ta yi wannan zargi ne sakamakon wasu rikice-rikicen shugabanci da jam’iyyar ke fama da shi, inda ta ce ana kokarin amfani da wannan dama domin hana ta shiga zabe.

ADC ta nuna damuwa cewa irin wannan yunkuri na iya kawo barazana ga tsarin dimokuradiyya, tare da tauye ‘yancin jam’iyyun siyasa na shiga zabe cikin gaskiya da adalci.

Sai dai, wasu bangarori sun bukaci jam’iyyar da ta bi hanyoyin doka wajen neman hakkinta idan tana ganin an tauye mata hakki, maimakon zargin hukumar zabe kai-tsaye.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use