Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa rikicin da ke faruwa a Iran ba ya nufin al’ummar ƙasar kai-tsaye, sai dai tsarin mulkin ƙasar wato Jamhuriyar Musulunci.
A cikin wani saƙo da ya wallafa, Gumi ya ce hare-haren da ake kai wa Iran suna nufin gwamnati da tsarin shugabanci, ne, ba talakawan kasar ba.
Ya ƙara da cewa, a fahimtarsa, al’ummar Farisawa ba su ne ake nufi da wannan yaƙi ba, illa dai tsarin siyasa da ake ganin yana haifar da rikice-rikice a yankin.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rikici da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya jawo muhawara daga bangarori daban-daban na duniya.
Sheikh Gumi ya jaddada bukatar bambance tsakanin gwamnati da kuma talakawan ƙasa yayin nazarin irin waɗannan rikice-rikice.