Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta tabbatar da cewa shugaban Bola Tinubu ya samu nasara a zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan ya yi wannan furuci ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Birnin Kebbi, inda ya ce sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar tare da cimma matsaya.
Ya jaddada cewa jam’iyyar APC ta samu karɓuwa sosai a jihar, yana mai cewa al’ummar Kebbi na goyon bayan jam’iyyar kuma za su sake ba ta nasara a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya a 2027.
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa ciki har da ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu, da sauran manyan shugabannin APC a jihar.
Gwamnan ya nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da riƙe madafun iko a jihar Kebbi da ma ƙasa baki ɗaya.