Majalisar dokokin jihar Kano ta janye shirin tsige Mataimakin gwamnan jihar Comrade Abdussalam Gwarzo, bayan da ya ajiye mukaminsa.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin janye tsige Abdussalam Gwarzo ya biyo bayan murabus ɗin da ya yi, wanda hakan ya kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya dabaibaye gwamnatin jihar.
Tun da farko dai majalisar ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan ne bisa wasu zarge-zarge, amma murabus ɗin sa ya dakatar da yunkurin.
Ana kallon wannan mataki a matsayin wani yunƙuri na kwantar da hankula da kuma dawo da daidaito a harkokin mulkin jihar Kano.