Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi kira ga matasan kasar da su tashi tsaye domin cin gajiyar fasahar AI, yana mai cewa bai kamata ƙasar ta zama mai kallo ba a wannan zamani na fasaha.
Shettima ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da wani shirin AI na AI University Innovation Pod (UniPod) a Jami’ar Lagos, inda ya jaddada cewa AI na daga cikin manyan fasahohin da za su sauya duniya da kuma buɗe hanyoyin ci gaba.
Shettima ya ce dole ne Najeriya ta gina ingantaccen tsarin fasaha da zai ba matasa, masana da kamfanoni damar samar da hanyoyin magance matsalolin ƙasa a fannoni kamar noma da lafiya da ilimi da kuma tattalin arziki.
Ya kuma ƙara da cewa burin gwamnati shi ne ba Najeriya ta zama mai amfani da fasahar AI kawai ba, said dai ma ta samar da sabbin dabaru da kirkire-kirkire a nahiyar Afirka.
Shugaban ya jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin jami’o’i da masana da masana’antu zai taimaka wajen shirya matasa domin su zama jagorori a sabon zamani na fasaha.