An samu tashin hankali yayin da zanga-zanga ta ɓarke a lokacin jana’izar wasu daga cikin waɗanda aka kashe a harin anguwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa na jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa matasa da mata sun mamaye wurin ibadar da ake gudanar da jana’izar, suna nuna rashin jin daɗi kan kama wasu matasa uku da jami’an tsaro suka yi, inda suka nemi a sake su kafin a ci gaba da jana’izar.
Zanga-zangar ta sa aka ɗan dakatar da jana’izar, yayin da yanayi ya rincabe sakamakon fargabar cewa an kama marasa laifi, maimakon bata-gari.
Sai dai daga bisani, a sake matasan da aka kama bayan matsin lamba daga al’umma.
Lamarin ya taimaka wajen kwantar da hankula da kuma ci gaba da gudanar da jana’izar cikin natsuwa.
An dai kai harin ne a ranar 29 ga Maris inda aka kashe mutane da dama, kuma adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa kusan 33 bayan wasu daga cikin waɗanda suka jikkata sun rasu.