Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Shugaban Lebanon ya yi Alla-wadai da hari mafi muni da Isra’ila ta kai

Shugaban Lebanon ya yi Alla-wadai da hari mafi muni da Isra’ila ta kai Shugaban Lebanon ya yi Alla-wadai da hari mafi muni da Isra’ila ta kai
Lamarin ya haifar da fargaba a yankunan da abin ya shafa (EPA)

Shugaban Lebanon, Joseph Aoun, ya yi Alla-wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai kasar da suka yi sanadiyyar kashe daruruwan mutane da kuma raunata wasu da dama.

Ya ce lamarin ya kara jefa tarihin Isra’ila cikin “mummunan hali” na take ‘yancin dan’adam.

A cikin wata sanarwa, Aoun ya ce “wadannan hare-haren mugaye ne wadanda ba su girmama hakki ko yarjejeniya, kuma sun nuna yadda Isra’ila ke watsi da doka da ka’idojin kasa da kasa baki-daya.

Shugaban ya kara da cewa “a cikin watanni 15 da suka gabata tun bayan yarjejeniyar dakatar da rikici a watan Nuwamba 2024, mun shaida irin laifukan da aka aikata ba tare da daukar hukunci ba.”

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use