Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa mutane miliyan 3.44 sun kammala rajistar zabe a zagaye na biyu na shirin yin rajista zuwa ranar 3 ga Afrilu.
Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa an samu karin masu rajista daga sassa daban-daban na Najeriya, ta hanyar rajista ta intanet da kuma ta kai-tsaye.
Daga cikin adadin, sama da mutane miliyan 2 sun kammala rajistar su ta intanetyayin da kusan miliyan 1.37 suka yi rajista a cibiyoyin yin rajista.
A bangaren jihohi, Jigawa ce ke kan gaba wajen yawan wadanda suka yi rajista, sai Legas na biyu, yayin da Kano ke matsayi na uku a jerin.
Rahoton ya kuma nuna cewa matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 su ne kan gaba wajen rajista, inda suka kai fiye da kashi 68 cikin 100 na sabbin masu rajistar zabe.