Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Shugaban APC ya soki jam’iyyun adawa kan rikice-rikicen cikin gida

Shugaban Jam'iyyar APC ta kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Shugaban Jam'iyyar APC ta kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda
Shugaban Jam'iyyar APC ta kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya soki jam’iyyun adawa bisa rikice-rikicen cikin gida da ke addabarsu, yana mai cewa hakan alama ce ta rashin shirinsu na jagorantar ƙasa mai girma kamar Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a birnin Abuja yayin da yake jawabi kan muhimman batutuwan da suka shafi siyasa, zamantakewa da tattalin arzikin ƙasa.

Ya jaddada cewa jam’iyyar da ba ta iya magance matsalolinta na cikin gida ba, ba za a iya amincewa da ita wajen jagorancin ƙasa ba.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Abimbola Tooki, ya fitar, Yilwatda ya bayyana cewa rikice-rikice, rarrabuwar kawuna, shari’o’i da faɗace-faɗace da ke faruwa a wasu jam’iyyun adawa na nuna raunin shugabanci da rashin tsari.

Ya ƙara da cewa miƙa ragamar mulki ga ‘yan siyasa da ba su iya tafiyar da jam’iyyunsu cikin tsari da daidaito ba na iya zama barazana ga makomar Najeriya, wadda ke buƙatar shugabanci nagari mai ƙarfi da hangen nesa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use