Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Yan bindiga sun kashe mutum biyar, tare da sace 22 a Sokoto

Wani ƙauye a Sokoto bayan harin ‘yan bindiga, inda ake nuna alamun tashin hankali da firgici a tsakanin mazauna yankin. Wani ƙauye a Sokoto bayan harin ‘yan bindiga, inda ake nuna alamun tashin hankali da firgici a tsakanin mazauna yankin.
Hare-haren ‘yan bindiga a Sabon Birni sun yi sanadin mutuwa da sace mutane da dama.

‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum biyar tare da yin garkuwa da wasu 22 a hare-haren dare da suka kai kan wasu ƙauyuka uku a ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sokoto.

Majiyoyi sun bayyana cewa an kai hare-haren ne tsakanin ƙarfe 11:00 na dare zuwa 12:00 na dare, inda aka kai farmaki a Sabon Birni, Dan Aduwa da Kwaren Gamba.

A garin Sabon Birni, maharan sun kutsa cikin gari ta wani ɓangare, inda suka riƙa harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.

An tabbatar da mutuwar mutane biyu, Abbas Sani da Bala Mai Laya Moriki, yayin da aka yi garkuwa da wasu takwas ciki har da wani makaho.

Haka kuma, an ruwaito cewa wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun fito ne daga Jihar Zamfara domin gudanar da harkokin kasuwancin kifi.

A halin yanzu, mutane biyar da suka jikkata na karɓar magani a asibiti, yayin da jami’an tsaro suka isa wurin bayan da maharan suka tsere.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use