Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Rikicin ADC: Nafiu Bala ya jagoranci zanga-zanga a Abuja

Masu zanga-zanga dauke da alluna suna yawo a titunan Abuja suna goyon bayan Nafiu Bala tare da suka kan wasu ‘yan siyasa. Masu zanga-zanga dauke da alluna suna yawo a titunan Abuja suna goyon bayan Nafiu Bala tare da suka kan wasu ‘yan siyasa.
Magoya bayan ADC sun fito zanga-zanga a Abuja suna goyon bayan Nafiu Bala tare da suka kan shugabannin adawa.

An gudanar da zanga-zanga a Abuja a ranar Alhamis karkashin jagorancin Nafiu Bala, inda masu zanga-zangar suka yi kira ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso da David Mark da su guji shiga jam’iyyar ADC.

Masu zanga-zangar sun zargi waɗannan manyan ‘yan siyasa da yunƙurin ƙwace jam’iyyar, suna mai cewa hakan na iya jefa ADC cikin rikici mai tsanani.

Nafiu Bala tare da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, sun jagoranci magoya baya dauke da alluna masu ɗauke da saƙonni daban-daban na goyon baya.

Wannan na zuwa ne bayan wata zanga-zanga da wani ɓangaren jam’iyyar da ake dangantawa da David Mark ya gudanar a hedikwatar INEC, abin da ke nuna rikicin shugabanci na ƙaruwa.

Lamarin ya nuna yadda rikicin cikin gida ke ƙara tsananta a jam’iyyar ADC, yayin da ɓangarori ke fafatawa kan makomar jam’iyyar a siyasar Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use