Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Amurka ta tura dakarun soji zuwa Najeriya
Aƙalla mutum biyar da jami’in soji sun mutu a harin ‘yan bindiga a Jihar Filato
An sako masu ibadar da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Aƙalla mutum biyar da jami’in soji sun mutu a harin ‘yan bindiga a Jihar Filato

Gwamnan jihar Filato ya sha fadin cewa yana aiki tukuru wajen magance matsalar tsaro (Hoto: Others) Gwamnan jihar Filato ya sha fadin cewa yana aiki tukuru wajen magance matsalar tsaro (Hoto: Others)
Gwamnan jihar Filato ya sha fadin cewa yana aiki tukuru wajen magance matsalar tsaro (Hoto: Others)

Aƙalla mutum biyar tare da wani jami’in soji sun rasa rayukansu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Wase, Jihar Filato.

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun kai harin ne cikin dare, yayin da mutane ke tsaka da barci, lamarin da ya haddasa firgici da tashin hankali a tsakanin al’umma.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki ne kan ƙauyukan Zurak da Sabon Gari da ke garin Bashar a daren Litinin, inda suka yi dirar mikiya da misalin ƙarfe 3:30 na dare. Ana zargin maharan da bude wuta tare da kona gidajen jama’a kafin su tsere.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mazauna yankin sun bayyana yadda suka shiga rudani sakamakon harbe-harbe da kuma barnar da aka yi wa dukiyoyinsu.

Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato domin ƙarin bayani bai yi nasara ba, domin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Alfred Alabo, bai amsa saƙonnin waya da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

A halin yanzu, ana ci gaba da jiran bayani kan jami’an soji uku da ake zargin sun ɓace yayin harin, ko za a same su lafiya ko a’a.

Idan za a iya tunawa, a ranar 21 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 28 da ke kan hanyarsu ta zuwa bikin Maulidi a ƙauyen Sabon Layi, a garin Bashar na Jihar Filato.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use