Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

A shirye muke don gwabza yaki na tsawon lokaci – Iran

Iran tace za ta iya shafe tsawon lokaci tana yaƙi ba tare da kakkautawa ba.

A yau Litinin yaki tsakanin Amurka-Isra’ila da Iran ke shiga rana ta 9, sai da a rahoton da kafar AP ta fitar ta ce Tehran na ci gaba da kai hare-hare kan wasu matsugunan Amurka da wasu sassa na birnin Tel Aviv har ma da ƙasashen yankin Gulf.

Duk da ita ma kasar Iran din na shan hare-hare ta ɓangarori da dama daga Isra’ilar, musamman kan asibitoci.

Sai dai ma’aikatar lafiya a Iran ta ce sashen lafiyar ƙasar na da ƙarfin da ba zai durƙushe ba duk irin hare-haren da Isra’ila ke kai masa, har ma da makarantun horas da likitoci da sauran jami’an lafiya.

Ya ce cibiyoyin lafiyar kasr suna da damar yin aiki a kashin kansu yayin da ma’aikatun samar da magunguna suka ƙara himma wajen samar da dukkanin magungunan da ake buƙata.

Ministan lafiya na Iran Ali Jafarian ya shaida wa manema labarai cewa kawo yanzu hare-haren Amurka-Isra’ila sun kashe mutane fiye da 1,255 ba ya ga jikkata wasu fiye da dubu 12.

Kazalika ministan lafiyar ya kara da cewa mutanen da hare-haren ke shafa sun fara ne daga watanni 8 zuwa shekaru 88 wanda ke nuna ƙasashen na Amurka da Isra’ila na kai harin ne kan mai uwa da wabi ba tare da la’akari da ƙananan yara ko kuma tsofaffi ba.

Bayanan ma’aikatar lafiyar ta Iran sun ce cikin mutanen da aka kashe har da mata 200, sai ƙananan yara 168 sai kuma jami’an lafiya 11 da suka ƙunshi likitoci 4 da malaman jinya 2 sai jami’an agaji guda 3.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use