Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa shi ma yana cikin manyan mutanen da aka tsara kai wa hari a yunkurin juyin mulkin da ake zargin wasu jami’an soji sun yi.
Wannan bayani na zuwa ne kwanaki bayan rundunar soji ta tabbatar da cewa wasu daga cikin jami’an soji 16 da aka kama tun watan Oktoban 2025 za su fuskanci shari’a bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Janar Musa, wanda shi ne tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin Sunday Politics na tashar Channels Television.
A hirar, Ministan tsaron ya ce masu shirin juyin mulkin sun yi niyyar kama shi, kuma idan ya ƙi amincewa da hakan, za a harbe shi.
Ya ce: “An shirya kama ni, kuma idan na ƙi, an shirya a harbe ni,”
Ya ƙara da cewa ba shi kaɗai ba ne aka sanya a jerin hare-haren, domin wasu manyan jami’an gwamnati da shugabanni ma an tsara kai musu farmaki.