Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Amurka ta gargadi ƴan kasarta mazauna Lebanon
ADC ta dage kan gudanar da tarukanta duk da gargadin INEC

ADC ta dage kan gudanar da tarukanta duk da gargadin INEC

ADC ta dage kan gudanar da tarukanta duk da gargadin INEC ADC ta dage kan gudanar da tarukanta duk da gargadin INEC
ADC ta dage kan gudanar da tarukanta duk da gargadin INEC

Jam’iyyar ADC ta yi martani mai zafi ga shugaban Hukumar Zaɓe a Najeriya INEC, Farfesa Joash Amupitan, kan gargadin da ya yi cewa gudanar da tarukan jam’iyyar na iya saɓa wa umarnin kotu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, jam’iyyar ta ce kalaman shugaban INEC sun nuna kuskuren fassarar umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara.

ADC ta kuma zargi INEC da wuce gona da iri a aikinta, tana mai cewa ba hurumin hukumar ba ne fassara umarnin kotu ko dakatar da ayyukan cikin gida na jam’iyya.

Jam’iyyar ta jaddada cewa babu wani umarni kai tsaye daga kotu da ya hana ta gudanar da taruka ko babban taronta na ƙasa, don haka za ta ci gaba da shirye-shiryenta bisa tanadin doka.

Haka kuma, ADC ta ce rikice-rikicen cikin gida ba sabon abu ba ne a tsarin dimokuraɗiyya, don haka bai kamata a yi amfani da su wajen dakatar da ayyukan jam’iyya ba.

Har ila yau, jam’iyyar ta yi gargadin cewa irin wannan mataki daga INEC na iya raunana tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya, tare da kira ga hukumar da ta tsaya kan aikinta na doka.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use