Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Rikicin ADC: Nafiu Bala ya jagoranci zanga-zanga a Abuja
ADC ta karɓi Marafa da magoya bayansa a Zamfara

ADC ta karɓi Marafa da magoya bayansa a Zamfara

ADC ta karɓi Marafa da magoya bayansa a Zamfara ADC ta karɓi Marafa da magoya bayansa a Zamfara
Jam’iyyar ADC a Jihar Zamfara ta karɓi tsohon sanata Kabiru Garba Marafa tare da dimbin magoya bayansa cikin jam’iyyar.

Jam’iyyar ADC a Jihar Zamfara ta karɓi tsohon sanata Kabiru Garba Marafa tare da dimbin magoya bayansa cikin jam’iyyar.

A wata sanarwa da jami’an jam’iyyar suka fitar, sun bayyana cewa shigowar Marafa babbar nasara ce da za ta ƙara ƙarfin jam’iyyar da haɗin kai a jihar.

Jam’iyyar ta yabawa Marafa, tana mai cewa gogewarsa a siyasa da jajircewarsa wajen yi wa al’umma aiki za su taimaka wajen ciyar da manufofin jam’iyyar gaba.

Haka kuma, ADC ta nuna farin ciki da yadda magoya bayansa da dama suka shiga tare da shi, tana mai cewa hakan na nuna amincewa da manufofin jam’iyyar na adalci, kyakkyawan shugabanci da kula da jama’a.

Jam’iyyar ta kuma tabbatar da cewa za a bai wa sabbin mambobin cikakkiyar dama da haɗin kai a harkokin jam’iyya, tare da ƙarfafa haɗin kai domin ci gaban Zamfara da Najeriya baki ɗaya.

Ana kallon wannan sauyi a matsayin wani muhimmin mataki a siyasar Zamfara gabanin zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use