Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

ADC ta kuduri aniyar ci gaba da zaɓukan cikin gida duk da takaddamar ta da INEC

Kakakin Jam'iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi Kakakin Jam'iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi
Kakakin Jam'iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi

Jam’iyyar ADC a Najeriya ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da gudanar da dukkanin zaɓukan cikin gida daga matakin gunduma har zuwa matakin ƙasa, duk da ce-ce-ku-ce da ke tattare da lamarin.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa sa ido da INEC ke yi a irin waɗannan zaɓuka ba wajibi ba ne.

Ya kuma jaddada cewa umarnin kotu bai cire kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da David Mark ke jagoranta ba.

Abdullahi ya ƙara da cewa tuni jam’iyyar ta sanar da INEC kan shirinta na gudanar da zaɓukan, kuma hukumar ta karɓa tare da tabbatar da samun sanarwar a hukumance.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use