Jam’iyyar hadaka ta ADC ta soki gwamnatin Bola Tinubu kan yadda Najeriya ta samu koma baya a rahoton matsayin tsaro na duniya na (Global Terrorism Index).
Jam’iyyar ta bayyana hakan a matsayin gazawa wajen kare rayukan ‘yan ƙasa da tabbatar da tsaro.
A wata sanarwa da Bolaji Abdullahi, Sakataren yada labarai na jam’iyyar, ya fitar, ADC ta ce rahoton na 2026 ya nuna cewa Najeriya ta tashi zuwa matsayi na huɗu a jerin kasashen da tashe‑tashen hankula da ta’addanci ya yi galaba akansu a duniya.
Rahoton ya bayyana samu mutuwar mutane 750 a shekarar 2025, karin kaso 46% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Jam’iyyar ta jaddada cewa wannan rahoto ba kawai lissafi ne ba, amma shaida ce ta raunana tsarin tsaro a ƙasar, inda hare‑haren ta’adda suka ƙaru, musamman a Borno State, inda fararen hula ke fi samun hasara.