Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Alƙali ya janye daga shari’ar EFCC da Malami

Abubakar Malami, Tsohon Ministan Shari'a a Najeriya.( Hoto: BBC)

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya janye kansa daga shari’o’i biyu da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar kan tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, a ranar Alhamis.

Alƙali Egwuatu, wanda babban alƙalin kotun tarayya, John Tsoho, ya sake ba shi shari’ar a kwanan nan, ya ce ya janye kansa daga shari’o’in ne saboda dalilai na kai-da-kai da kuma tabbatar da adalci.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use