Mai shari’a Obiora Egwuatu ya janye kansa daga shari’o’i biyu da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar kan tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, a ranar Alhamis.
Alƙali Egwuatu, wanda babban alƙalin kotun tarayya, John Tsoho, ya sake ba shi shari’ar a kwanan nan, ya ce ya janye kansa daga shari’o’in ne saboda dalilai na kai-da-kai da kuma tabbatar da adalci.