Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amaechi ya bi sahun masu zanga-zanga kan dokar zabe

Yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar ce-ce-ku-ce kan gyaran dokar zaɓe, musamman tanade-tanaden da suka shafi tura sakamakon zaɓen ta intanet wasu fitattun ‘yan Najeriya na kara shiga zanga-zangar neman a yi daidai.

Na baya-bayan nan daga cikin wadanda suka bi sahun masu zanga-zangar shi ne tsohon ministan sufurin kasar Rotimi Amaechi.

An hangi tsohon gwamnan Jihar ta Ribas kuma jigo a jam’iyyar ADC cikin masu zanga zangar da ke wakana a zauren shiga majalisar ta dokoki.

A cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an hangeshi tare da sauran masu zanga zanga yana karfafa musu guiwa.

Daga cikin masu zanga-zangar akwai gamayyar kungiyoyin fararen hula da na matasa da kuma masu rajin kishin dimokuradiyya da kuma jam’iyyun adawa.

Idan za’a iya tunawa dai, a jiya Litinin shima dan takarar shugaban kasa a tutar jam’iyyar Labour Party Peter Obi da ‘yar gwagwarmaya Aisha Yesufu sun bi sahun masu zanga-zangar.

Ko da yake shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yi kiran zaman gaggawa a yau Talata don tattauna batutuwan da suka tayar da zanga-zangar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use