Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adam ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike cikin gaggawa kan kashe wata yarinya a birnin Maiduguri na jihar Borno da suke zargin sojojin ƙasar da aikatawa.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce an kashe yarinyar ce mai shekara 14 ranar Asabar 4 ga watan Maris, bayan harsashi ya same ta a cikin gidansu lokacin da sojoji ke harbin bindiga a wani ɓangare na nuna murnar wani bikin aure.
“Marigayiyar na zaune ne cikin rukunin gidaje na asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri tare da iyalanta, kuma tana cikin gida lokacin da harsashin ya same ta. Kuma ta kammala yi wa mahaifiyarta da kanta lalle don wani bikin ƴan uwansu da za a yi kenan lamarin ya faru,” kamar yadda sanarwar Amnesty ta bayyana.
Tuni kuma aka yi jana’izarta a safiyar yau a birnin Maiduguri.
Amnesty ta yi kiran gudanar da cikakken bincike ba tare da son rai ba don tabbatar da adalci ga dangin yarinyar.