Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka da Iran na dab da fara tattaunawa a Pakistan

Shirin ganawar Amurka da Iran a Pakistan ya janyo rudani kan halartar JD Vance Shirin ganawar Amurka da Iran a Pakistan ya janyo rudani kan halartar JD Vance
Tattaunawar Amurka da Iran a Pakistan na fuskantar cece-kuce kan halartar manyan jami’ai, ciki har da JD Vance.

Tawagogi daga Amurka da Iran na shirin isa Pakistan a ranar Juma’a domin gudanar da wata muhimmiyar tattaunawa, kamar yadda Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya bayyana.

Sai dai rahotanni sun ce akwai rashin daidaito kan jerin mutanen da za su halarci wannan ganawa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaton wasu majiyoyi biyu daga Pakistan da ba a bayyana sunayensu ba, na cewa mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ne zai jagoranci tawagar Amurka, kuma zai gana da Kakakin Majalisar Dokokin Iran da kuma Ministan Harkokin Wajen Iran a birnin Islamabad.

A wani bangare kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana wa kafafen yada labaran kasar cewa tattaunawar kai-tsaye da Iran za ta gudana nan ba da jimawa ba.

Ya kuma yi nuni da cewa JD Vance na iya rashin halartar wannan ganawa saboda dalilai na tsaro.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use