Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon na shirin tura sojojin ƙasar zuwa Iran don yin yaƙi ta ƙasa na makonni ciki har da yiwuwar kai samame a Kharg Island.
Jaridar Washington Post ta ce shirin ba na mamaya ba ce gaba daya, amma ya kunshi kai samame na musamman ta kasa da kuma yin gumurzu da sojojin Iran.
Ba a tabbatar ko Shugaba Trump zai amince da waɗannan shirye-shiryen ba, in ji fadar White House.
Gwamnatin Trump ta riga ta tura sojoji sama da dubu uku Gabas ta Tsakiya, sannan tana shirin tura wasu dubbai daga rundunar 82nd Airborne zuwa yankin a shirye-shiryen da take yi na far wa Iran ta kasa.