Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Amurka na shirin kai wa rumbun uranium din Iran hari’

Gwamnatin Trump na kokarin kai hari ta ƙasa don ƙwace iko da rumbun Uranium na Iran da aka habaka wanda Amurkan ke tunanin an boye shi a can karkashin kasa a cibiyar sarrafa nukiliya ta Iran da ke Isfahan.

Da yake ganawa da gidan talabijin na CNN, wani jami’in sojin Amurka Rafael Grossi, ya ce, kasar sa na kyautata zaton an ɓoye uranium din da aka inganta da haɓakawa a can karkashin kasa a cibiyar sarrafa nukiliya ta Iran da ke Isfahan.

Jami’in ya ce matakin da shugaban Amurka Donald Trump ke son ɗauka na ƙwace tarin uranium din zai buƙaci kasancewar sojojin ƙasa na Amurka a can ba wai kawai aikin soji na sama kadai ba.

Ya kara da cewa, kwace su zai yi daidai da umarnin Trump na kawar da ƙarfin nukiliya na Iran gaba ɗaya, wanda shi ne ɗaya daga cikin manufofin shugaban ƙasar na fara yaƙin.

Kwararrun sojoji sun ce idan gwamnatin Trump ta ci gaba da aikin kwace uranium din, zai iya zama babban aikin farko na sojojin ƙasa na Amurka a yaƙin.

Wannan shirin da Trump ke yi, zai zama wani matakin soja da zai sanya mafi yawan sojojin kasar Amurka cikin hatsari a cewar masana tsaro.

Tun da fari dai Trump ya sha alwasin hana Iran mallakar makamin nukiliya saboda acewar sa ta fi kowace kasa tallafa wa ta’addanci.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use