Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka na son dakatar da yaƙi da Iran – Trump

WASHINGTON, DC - MARCH 04: U.S. President Donald Trump speaks during a roundtable meeting on the administration's "ratepayer protection pledge" in the Indian Treaty Room at the White House on March 04, 2026 in Washington, DC. The pledge is a policy designed to shift rising energy costs from artificial intelligence data centers away from consumers. (Photo by Win McNamee/Getty Images)

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a daren Litinin cewa suna duba yiwuwar kawo ƙarshen yaƙi da ƙasar ke yi da Iran.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da shugaban ke fuskantar suka a cikin gida kan wannan yaƙi da kashi mai yawa na Amurkawa ba sa goyon baya.

Trump ya bayyana cewa Amurka ta cimma dukkanin muradanta an Iran tun a kwanakin farko na yaƙin, don haka babu amfanin ci gaba da gwabza fada.

Sai dai kalaman na zuwa a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan Tehran.

Jim kadan bayan jawabin Trump, shugaban ya sake aika gargaɗi ga Iran bayan da ya yi barazanar ragargazar ƙasar fiye da abin da ya yi mata a yanzu muddin ta ci gaba da tare jiragen ruwa a mashigin Hourmuz.

Matsin lamba ya yi wa Amurka yawa ta ɓangarori da dama, ciki har da ƙawayenta na Gulf da ke ganin kai tsaye Amurkan ta kai musu yaƙi ba kuma tare da ba su kariya ba, lura da yadda ta tattara ƙarfinta wajen bai wa Isra’ila tsaro.

Sai dai duk da kalaman Trump da ke nuna yiwuwar dakatar da yaƙin nan kusa, Iran ta mayar da martani inda ta ce ba Amurka ke da ikon iya sanar da lokacin kawo ƙarshen yaƙin ba, domin a shirye ƙasar ta ke a ci gaba da gwabzawa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use