Gwamnatin Amurka ta bakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da hare-haren da suka faru a Jos, Jihar Filato, tana mai bayyana su a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.
A cikin wata sanarwa, Amurka ta bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta gaggauta ɗaukar matakai masu ƙarfi domin inganta tsaro da kare rayukan jama’a, musamman a wannan lokaci na bukukuwan addini.
Haka kuma, jami’an Amurka sun nuna damuwa kan yadda ake kai hare-hare kan fararen hula, tare da kira ga hukumomin Najeriya su ƙara ƙaimi wajen dakile tashin hankali da kuma gurfanar da masu hannu a hare-haren gaban kuliya.
Rahoton ya kuma nuna cewa wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar, inda hare-hare ke ƙara yawaita, musamman a yankunan Arewa da tsakiyar Najeriya.