Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka ta ce an ceto matuƙin jirginta da ya ɓace a Iran

Trump na shirin daukar mataki mai hadari ga Amurka ko Iran Trump na shirin daukar mataki mai hadari ga Amurka ko Iran
Trump ya ce aikin ceton ya kasance ɗaya daga cikin mafi jarumta a tarihin Amurka (Reuters)

Shugaban Donald Trump na Amurka ya ce sojojin ƙasar sun ceto matuƙin jirgin yaƙin ƙasar da ya ɓace a kudancin Iran, bayan harbo jirginsa a ranar Juma’a.

Wata sanarwa da Mista Trump ya wallafa a kafofin sada zumunta, ya ce sojojin sun gudanar da aikin ceto mafi jarumta a tarihin Amurka.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi mummunan artabu tsakanin sojin Amurka da kuma na Iran a lokacin aikin.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a kafofin sada zumunta sun nuna yadda ɗaruruwan mutane ke tururuwar zuwa yankin mai tsaunuka a kudu maso yammacin Iran don taimakawa wajen gano inda sojan yake.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use