Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka ta tuntuɓi mayaƙan Kurɗawa kan yiwuwar kai wa Iran farmaki ta ƙasa

Jagoran wata ƙungiyar mayaka ‘yan kishin ƙasa ta Kurdawa da ke zaune a yankin Kurdistan na arewacin Iraki mai cin gashin kansa ya shaida wa Al Jazeera cewa akwai yiwuwar Kurdawan Iran su kaddamar da hari ta ƙasa daga kan iyaka zuwa cikin Iran.

Babasheikh Hosseini, babban sakataren ƙungiyar Kurdawan a yankin Kurdistan, ya ce a halin yanzu ba a kai wani farmaki ba, amma Amurka ta riga ta tuntubi ƙungiyar, kuma suna nazarin yiwuwar fara kai hare-hare.

Hosseini ya bayyana cewa sun dade suna shirye-shiryen wannan mataki, kuma a yanzu da dama ta samu, akwai yiwuwar fara kai farmaki.

Jagoran ‘yan tawayen ya kuma bayyana cewa Amurkawa sun tuntube su ta hanyoyi daban-daban, ko da yake har yanzu ba su gana kai tsaye ba, amma dai ya tabbatar da cewa an tattauna da su.

A gefe guda kuma, rundunar juyin-juya- hali ta Iran ta sanar a ranar Asabar dinnan cewa ta kai hare-hare kan wuraren da ta kira kungiyoyin masu neman ballewa a yankin Kurdistan, inda ta yi gargadin cewa idan irin wadannan kungiyoyin suka yi wani yunkuri da zai yi barazana ga ikon Iran, za ta murkushe su gaba daya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use