Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

An girke jami’an tsaro a harabar kotun da za a yi El-Rufa’i shari’a a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa tuni aka isa da tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru El-Rufa’i babban kotun tarayya da ke jihar Kaduna domin fuskantar tuhume-tuhumen da hukumar ICPC da ma wasu hukumomin kasar ke masa.

An tsare El-Rufa’i bayan amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi masa, inda ta tsare shi na tsahon awanni 48 kafin daga bisani ita ma hukumar ICPC ta kama tare da tsare shi har zuwa yau da za a gurfanar da shi gaban kotu.

An dai jima ana kira-kiraye ga hukumar ICPC kan ta wanke El-Rufa’i bisa zarge-zargen da take masa ko ta gurfanar da shi a gaban kotu.

Ana zargin El-Rufa’i da almundahana tare da karkatar da wasu kadarorin al’ummar jihar lokacin da yake mulki.

Tuni aka girke jami’an tsaro a ciki da wajen babban kotun tarayya da ke jihar kafin fara sauraron shari’ar Nasiru El-Rufa’i.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use