Kafofin yada labaran Iran sun bayyana cewa an kai wa tashoshin makamashin kasar hari.
Rahotanni daga Iran sun ce kasashen Amurka da Isra’ila sun kai wa tashoshin makamashin Iskar gas na kasar hari, sa’o’i kadan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya janye kudurinsa na kai wa tashoshin makamashin kasar hari.
Rahoton ya kara da cewa ‘hare haren da Amurka da Isra’ila suka kai sun hadar da gine-ginen hukumar gudanarwar tashoshin da tashar da ake tace Iskar gas din da ke kan hanyar Kaveh a yankin Isfahan’
Kamfanin dillancin labaran kasar, Fars Newa, ya ce hare-haren sun barnata ababen amfani da dama na tashoshin, kazalika harin ya lalata bututun isar da iskar gas da ke yankin Khorramshahr da ke yammacin Iran.