Kungiyar kare hakkin dan’adam ta Amnesty International ta ruwaito cewa an kashe mutum sama da 323 a cikin kwanaki 20 a arewacin Najeriya.
Amnesty ta ce mutanen sun mutu ne bayan jerin hare-hare da ‘yanbindiga suka kai jihohi shida na arewacin kasar da suka hada da Benue, Katsina, Kwara, Kebbi, Neja da kuma Zamfara a cikin kwanaki 20 na farko na watan Fabrairu.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na X, ta ce yawan hare-hare da ake kai wa sun nuna karara gazawar gwamnati na kawo karshen matsalar rashin tsaro da kungiyoyi masu rike da makamai ke haddasa wa na tsawon shekaru.
A cewar kungiyar, ci gaba da kai hare-hare da kuma rashin hukunta masu aikata laifin na barazana ga ‘yancin rayuwa a Najeriya.
“‘Yanbindiga kan babura na afka wa garuruwa inda suke bude wuta kan al’ummomi, garkuwa da mata da ‘yanmata, kona gidaje da satar dabbobi da kuma lalata amfanin gona,” in ji Amnesty.
Don haka ta ce ya zama dole gwamnatin Najeriya ta tashi don kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma.