Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

An samu karancin masu kada kuri’a a zaben cike gurbi a Kano

Zaben cike gurbi/INEC/Facebook

An samu karancin fitowar masu yin zabe a zabukan cike gurbi na Majalisar Dokokin jihar Kano a ranar Asabar.

Ana gudanar da zaben ne a rumfuna 1,014 da ke cikin yankuna 24, bayan rasuwar ‘yan majalisa biyu wato Aminu Sa’ad Ungogo na mazabar Ungogo da Sarki Aliyu na mazabar Kano Municipal a watan Disambar 2025.

Ana sa ran kimanin masu kada kuri’a 535,000 da suka yi rajista za su yi zaben. Rahotanni sun nuna cewa kayan zabe sun isa rumfunan zabe da wuri.

Sai dai jami’ai da wasu mazauna yankunan sun nuna damuwa kan karancin fitowar jama’a, duk da cewa suna ganin yawan masu kada kuri’a zai karu yayin da rana ke kara yi.

Rahotanni daga sassa daban-daban na mazabun sun nuna cewa ana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, ba tare da samun wata babbar matsala ba.

Hukumomin tsaro sun baza jami’ansu domin tabbatar da zaman lafiya, yayin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sake jaddada kudurinta na gudanar da sahihin zabe.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use