Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta sanar da takunkumi na awanni 18 a Kano Municipal da Ungogo ranar Asabar, domin zaben cike gibi na majalisar jihar.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan ga manai ma labarai a madadin kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Kano inda ya ce umurnin ya biyo bayan taron bitar tsaro da kwamitin hadin gwiwa kan tsaron zabe ya gudanar.
Takunkumin zai fara daga karfe 12:00 na tsakar dare har zuwa 6:00 na yamma, kuma ya shafi dukkan motoci, babur, da kekuna. sai motoci masu aikin gaggawa kamar na asibitoci, kashe gobara, jami’an zabe da masu lura da zabe aka yarda su yi aiki.
Rundunar ta ce kwamitin ya kammala tsara yadda jami’an tsaro za su rarraba kansu da kuma dabarun haɗin gwiwa domin hana duk wata tashin hankali a lokacin zabe.
Baya ga takunkumin motsi, kawai masu kada kuri’a da wakilan jam’iyyun da hukumar INEC ta tantance ne za a yarda su shiga wuraren zabe.
Rundunar ‘yan sandan Kano ta yi kira ga mazauna jiha da su bi wannan umurni domin tabbatar da tsaro da gudanar da zabe cikin tsari da lumana.