Wani malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi, ya yi Alla-wadai da abin da ya bayyana a matsayin hauhawar farashi mara da’a da ‘yan kasuwa suka yi a Kano, musamman bayan gobarar da ta afku a kasuwar Singer a kwanakin nan.
Idan ba’a manta ba dai ‘yan kasuwa a shahararriyar kasuwar Singer sun gamu da iftila’in gobara har sau biyu mabam-banta, wanda ya haifar da asarar kayayyaki da darajarsu ta kai biliyoyin naira.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Farfesa Kurfi ya bukaci ‘yan kasuwa da su ji “tsoron Allah” yayin da yake tunatar da su alhakin da ya rataya a wuyansu na ɗabi’a, musamman a wannan watan na Ramadan mai tsarki, lokacin da ya kamata a bai wa walwalar ‘yan ƙasa fifiko.
“An nuna tausayi ga ‘yan kasuwar Singer har da yi musu addu’o’i, da tallafin kuɗi daga gwamnatocin tarayya da na jihohi da kuma ‘yan siyasa. Duk da haka, maimakon rage wa mutane sauki, wasu sun koma ƙara farashin kayayyaki,” in ji Farfesa Kurfi.
Tsohon shugaban sashen tsangayar aikin jarida na Jami’ar ta Bayero, ya nuna damuwa kan cewa irin wannan halayyan yana nuna irin cin zarafin ‘yan ƙasa a lokacin da ya kamata a taimake su.