An tsinci gawar mataimakin sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Abdulsalami Ginsau, a elebeto wani otel a Abuja da ke yankin Utako a babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa marigayin yana daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen shirya wani taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa Ginsau ya rasu ne sakamakon makalewa a wata na’ura ta otel ɗin.
Haka kuma, bincike ya nuna cewa Abdulsalami Ginsau ya rasu tun ranar 27 ga watan Maris da ya gabata.