Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ana fargabar ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 150 a Zamfara

'Yan bindiga

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun ce ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Bukuyum, inda suka kashe mutum 7 tare da sace mutane da dama.

Harin ya shafi ƙauyen Kurfa da wasu yankunan da ke kewaye da shi, inda mazauna suka ce ‘yan bindiga da dama sun kutsa tare da yin harbe-harbe ba kakkautawa.

Wasu majiyoyi sun nuna cewa adadin waɗanda aka sace na iya haura mutum 150, duk da cewa har yanzu ba a samu cikakken bayanin hukumomi kan ainihin adadin ba.

Mazauna yankunan da abin ya faru ne dai suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP faruwar lamarin, inda suka ce harin ya jefa su cikin firgici.

Rundunar ƴansandan Jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a yau Asabar, inda ta ce an kai harin ne a ranar Alhamis, sai dai ba ta ba bayyana adadin waɗanda abin ya shafa ba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use