Sama da mutum 70 ne suka bata bayan da wani jirgin ‘yan ci-rani ɗauke da mutum 105 ya kife a tekun Libya.
Cikin mutanen da jirgin ya kife da su har da yara.
Sai dai, an samu nasarar ceto mutum 32 da kuma gawawwaki biyu, a cewar wata kungiyar ceto a teku.
Ɗaruruwan ‘yan ci-rani ne da ke tsallakawa zuwa Turai don samun rayuwa mai inganci ke mutuwa a kowace shekara a cikin teku.