Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ana yaƙi ne da tsarin mulkin Iran, ba da mutanen kasar ba – Sheikh Gumi

Ana yaƙi ne da tsarin mulkin Iran, ba da mutanen kasar ba - Sheikh Gumi Ana yaƙi ne da tsarin mulkin Iran, ba da mutanen kasar ba - Sheikh Gumi
Ana yaƙi ne da tsarin mulkin Iran, ba da mutanen kasar ba - Sheikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa rikicin da ke faruwa a Iran ba ya nufin al’ummar ƙasar kai-tsaye, sai dai tsarin mulkin ƙasar wato Jamhuriyar Musulunci.

A cikin wani saƙo da ya wallafa, Gumi ya ce hare-haren da ake kai wa Iran suna nufin gwamnati da tsarin shugabanci, ne, ba talakawan kasar ba.

Ya ƙara da cewa, a fahimtarsa, al’ummar Farisawa ba su ne ake nufi da wannan yaƙi ba, illa dai tsarin siyasa da ake ganin yana haifar da rikice-rikice a yankin.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rikici da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya jawo muhawara daga bangarori daban-daban na duniya.

Sheikh Gumi ya jaddada bukatar bambance tsakanin gwamnati da kuma talakawan ƙasa yayin nazarin irin waɗannan rikice-rikice.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use