Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

APC ta karyata Jita‑jitar Gwamna Bala Mohammed zai shiga cikin ta

Jam’iyyar APC reshen Jihar Bauchi ta ce ba ta samu wani tabbaci a hukumance daga Gwamna Bala Mohammed na PDP kan jita‑jitar cewa zai bar PDP zuwa APC ba.

Shugaban jam’iyyar na jihar Bauchi, Muhammad A. Hassan Tilde, ya bayyana cewa duk rahotannin da ake yadawa suna nan a matsayin jita‑jita kawai.

Tilde ya kara da cewa idan gwamnan ya yanke shawarar shiga APC, dole ne a bi tsarin da jam’iyya ta gindaya daga matakin ƙaramar hukuma har zuwa matakin jiha.

A halin yanzu, APC ta ce tana nan a shirye ta karɓi gwamnan idan ya nuna aniyarsa ta shiga jam’iyyar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use