Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

APC ta soki bukatar ADC na murabus ɗin shugaban INEC

Jam’iyyar APC ta musanta zargin da jam’iyyar ADC ta yi na cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na da hannu wajen rikicin shugabanci da ke addabar ADC, wanda ya sa aka nemi Shugaban INEC ya yi murabus.

A jawabin da ya yi a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, sakataren APC na ƙasa, Ajibola Basiru, ya bayyana cewa wannan zargi bai da tushe.

Ya ce kalaman ADC ba komai bane illa ƙoƙarin ɓoye matsalolin cikin gida na jam’iyyar.

Basiru ya ƙara da cewa zargin cewa Shugaba Tinubu na raunana jam’iyyun adawa domin kafa tsarin jam’iyya ɗaya kafin zaɓen 2027 ba shi da tushe kuma ya saba wa kundin tsarin mulki.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use