Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Atiku ya kai ziyarar jaje ga El’rufa’i bayan yunkurin kama shi

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-rufa’i bayan yunkurin kamashi da jami’an tsaro suka yi a filin jirgin sama na babban birnin Najeriya Abuja.

Yunkurin na kama tsohon gwamnan na Kaduna ya faru ne kwana guda bayan ya zargi gwamnatin Tinubu da shirya makarkashiya ga ‘yan adawa mussaman irinsa da ke fada gwamnatin a fili.

Ziyarar tasa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya ce ta girmamawa ce ga tsohon gwamnan na Kaduna kuma jigo a Jam’iyar hadaka ta ADC.

Kafun yunkurin kamashi, Mallam Nasir Elrufai ya jadda cewar duk wata hukumar ta ke sha’awar gayyatarsa kofa a bude ta ke idan ta bi tsarin da doka ta shinfida.

El-rufa’i ya fada wa BBC cewa, yayi nadamar tallata gwamnatin Tinubu sabi da haka ne ya ce yake son tabbatar da korar gwamnatin daga mulki domin gyara kuskuren da ya yi a baya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use