Ƙasar Austria ta ce ba za ta amince da buƙatar Amurka ta amfani da sararin samaniyyarta wajen kai hare-hare kan Iran ba, tana mai jingina hakan da manufofinta na rashin shiga rikicin soja, a cewar Ma’aikatar Tsaron ƙasar.
Wakilin ma’aikatar ya bayyana cewa Amurka ta gabatar da buƙatu da dama, amma bai fayyace adadinsu ba. Ya ƙara da cewa ana duba kowanne buƙatu ne daban-daban tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Austria kafin yanke hukunci.
A wani ɓangare na Turai, Spain ma ta rufe sararin samaniyyarta ga jiragen sojan Amurka da ke da alaƙa da rikicin, inda ta nuna rashin goyon bayanta ga yaƙin. Haka kuma, gwamnatin Italiya ta ƙi bai wa Amurka izinin amfani da wani sansanin soji a Sicily ga jiragen yaƙi a makon da ya gabata.