Saudiyya ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba, inda za a cika azumi 30.
Wata sanarwa a shafin Haramain ta ce hakan na nufin cewa sai ranar Juma’a za a yi idin karamar sallah.
Sai dai a Najeriya, Musulmi na jiran sanarwa daga Sarkin Musulmi wanda ke da alhakin tabbatar da ranar Sallah bayan karɓar rahotannin ganin wata daga sassa daban-daban na ƙasa.