Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio, ya ce majalisar ba ta yi watsi da tsarin tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba a garanbawul da suka yi wa dokar zaɓen ƙasar ta 2022.
Akpabio ya bayyana haka ne yayin jawabi a wurin ƙaddamar da wani littafi a Abuja a ranar Asabar, inda ya ce ba a haramta tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba, sai dai an cire wurin da aka ce tura sakamakon zaɓen “kai-tsaye”.
Ya ƙara da cewa “Abin da muka ce shi ne a cire ɓangaren da ya ce ‘kai-tsaye’, domin idan aka ce haka to akwai batun matsalar network inda ba za a iya tura saƙo ba.
Akpabio ya ce an ɗauki matakin ne domin bai wa hukumar zaɓe ta INEC damar zaɓar hanyar da ta fi dacewa wajen aika sakamakon zaɓe, tare da la’akari da matsaloli da ake samu a ɓangaren fasaha da kuma tsaro.
Tun da farko dai, ƴan adawa da ƙungiyoyi sun yi ta sukar majalisar kan rashin amincewa da gyaran sashen da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura.