Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ba za mu sa taƙunƙumi kan kafafen sada zumunta ba – Gwamnan Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya musanta jita-jitar cewa gwamnatinsa na shirin kafa doka domin sanya ido ko takaita abubuwan da ake wallafawa a kafafen sada zumunta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi manyan shugabannin kafafen yaɗa labarai a gidan gwamnati da ke Kano, yayin wani taron buɗa baki na watan Ramadan.

Ya ce duk da cewa gwamnati ba ta da niyyar takaita ‘yancin faɗar albarkacin baki, amma ana bukatar mutane su riƙa amfani da kafafen sada zumunta cikin ladabi da mutunta juna.

Shi ma Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Abdullahi Ibrahim Waiya, ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnati da kafafen yaɗa labarai, yana mai cewa ‘yan jarida su ne ginshiƙin dimokuraɗiyya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use