Hukumar Zaben Najeriya (INEC) ta ja hankalin jama’a kan wani labari da ake yaɗawa a intanet da ke nuna cewa hukumar tana daukar aiki.
INEC ta bayyana labarin a matsayin karya da kuma yaudara.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, hukumar ta bayyana cewa ba ita ce ta amince ko ta ƙirƙiri hanyar (link) da ake amfani da ita ba dangane da zargin daukar ma’aikata.
INEC ta jaddada cewa shafin yanar gizon na bogi ne, kuma ba ya wakiltar duk wani shiri na hukumar game da daukar ma’aikata da ta keyi.
Hukumar ta kuma shawarci jama’a da kada su cika ko su tura bayanan sirri ko wasu muhimman bayanai a wannan dandali na ƙarya, tana mai gargadin cewa hakan na iya jefasu su ga zamba da damfara.
INEC ta ƙara da cewa duk wata sanarwa ta hukuma game da daukar ma’aikata da sauran bayanai masu alaƙa za a fitar da su ne kawai ta shafinta na yanar gizo da aka tabbatar da sahihancinsa da kuma hanyoyin sadarwa da aka amince da su.