Tsohon ministan sadarwar Najeriya, Isa Ali Pantami ya musanta zargin cewa ya taɓa faɗin shiga siyasa haramun ne.
Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da BBC Hausa.
”Ban taɓa cewa shiga siyasa haramun ne ba, idan akwai wanda ya taɓa ji ina so ya kawo min wurin,” in ji shi.
Ya ce ya shiga siyasa ne domin kawo shugabanci na gari ga al’umma.
”Abin da ake nufi da siyasa shi ne shugabanci nagari, don haka duk mutum mai nagarta na da sha’awar samar da shugabanci nagari”, in ji Pantami.
Sheikh Pantami ya ce ya jima da shiga siyasa, kuma a matsayinsa na ɗan Najeriya kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi damar shiga harkokin siyasar ƙasar.