Kungiyar Barcelona ta samu gagarumar nasara bayan doke Atletico Madrid da ci 2-1, wanda ya kara mata karfi a saman teburin gasar La Liga.
Atletico ce ta fara cin kwallo ta hannun Giuliano Simeone, amma Marcus Rashford ya farke wa Barcelona kafin a tafi hutun rabin lokaci kamin Daga bisani, Robert Lewandowski ya zura kwallon nasara a karshen wasa.
An kuma kori dan wasan Atletico, Nico Gonzalez, a farkon rabin wasa na biyu, lamarin da ya bai wa Barcelona damar mamaye wasan.
Wannan nasara ta sa Barcelona ta bude tazarar maki 7 tsakaninta da Real Madrid, abin da ke kara kusantar da ita da lashe kofin gasar bana.
Sakamakon na nuna cewa Barcelona na da kyakkyawar dama ta lashe gasar yayin da ake daf da karshen kakar wasa.